Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fursunoni 22 sun tsere daga gidan kaso a Kamaru
2019-08-09 11:01:43        cri
Fursunoni akalla 22 ne suka tsere da safiyar jiya Alhamis, daga wani gidan kaso dake garin Meiganga mai tsaunika, wanda ke yankin Adamawa a Jamhuriyar Kamaru.

'Yan sanda sun ce fursunonin sun yi nasarar haka rami a jikin bangon gidan kason, wanda ya ba su damar arcewa da misalin karfe 4:30 na safe, agogon wurin.

A cewar 'yan sandan, tuni aka kaddamar da farautar mutanen da suka tsere.

Tun a watan Janairun bana matsalolin sace-sacen mutane da kashe-kashe suka addabi yankin, lamarin da ya sanya shugaban kasar Paul Biya, tura dakarun musammam zuwa yankin, domin tabbatar da doka da oda.

An kama wasu daga cikin masu satar mutanen inda kuma aka tura su gidan kaso. Sai dai abun da ba a kai ga ganowa ba shi ne, ko masu satar mutanen na daga cikin wadanda suka tsere. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China