Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin yankin Hong Kong ta yi Allah wadai da masu zanga-zanga masu tsattsauran ra'ayi
2019-09-30 12:31:50        cri
Kakakin gwamnatin yankin musamman na Hong Kong, ya yi Allah wadai da kakkausar murya, kan ayyukan karya doka da masu zanga-zanga masu tsattsauran ra'ayi suka yi a jiya Lahadi.

Kakakin ya ce a jiyan, wasu masu zanga-zanga sun taru a wuraren Causeway Bay, da Wan Chai, da kuma Admiralty, inda suka bata yanayin sufuri a yankuna da dama, har ma sun cinna wuta a wurare da dama, da kuma jefa boma-bomai na man fetur ga ofisoshin 'yan sanda dake tashar jirgin kasa ta MTR, da Mong Kok, lamarin da ya kawo babbar barazana ga yanayin tsaro da 'yan sandan wurin, da ma'aikatan MTR da kuma mutanen wurin ke ciki.

Rundunar 'yan sandan Hong Kong ta fidda sanarwa a safiyar yau cewa, matakan tashe-tashen hankulan da masu zanga-zanga suka dauka, sun bata yanayin tsaro na 'yan sanda, da ma mutanen Hong Kong, don haka sanarwar ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan wannan lamari. Ta kuma jaddada cewa, ba za ta yi hakuri kan ko wane mataki na tada hankali ba. Kana za ta cafke wadanda suka aikata wannan laifi, domin kiyaye tsaron yankin Hong Kong. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China