Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci Amurka da ta daina tsoma baki cikin harkokin Hong Kong
2019-09-19 19:38:51        cri

A Alhamis din nan ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya sake bayyana matsayin gwamnatin kasar Sin kan batun Hong Kong, inda ya bukaci Amurka da ta daina tsoma baki a cikin harkokin yankin Hong Kong nan take.

An ce, kwanan baya shugabar majalisar wakilai ta Amurka Nancy Pelosi, ta kira taron ganawa da manema labarai kan batun "dokar hakkin dan Adam da demokuradiya ta Hong Kong ta shekarar 2019", inda ta gayyaci Joshua Wong, da Denise Ho, da sauran masu ra'ayin neman 'yancin Hong Kong domin halartar taron. Kana Pelosi ta bayyana cewa, majalisar wakilai da ta dattijan Amurka, sun nuna goyon bayansu ga dokar.

Geng Shuang ya yi nuni da cewa, 'yan siyasar Amurka ciki har da Pelosi, sun kira taron ganawa da manema labarai a fili, domin fitar da dokar dake shafar yankin Hong Kong. Inda har suka yi cudanya da masu ra'ayin neman 'yancin Hong Kong. A hannu guda kuma, sun rika tsoma baki a cikin harkokin gidan kasar Sin kamar yadda suke so, al'amarin da kasar Sin ta yi adawa da shi. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China