Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin yankin musamman na Hong Kong ta yi Allah wadai da ayyukan nuna karfin tuwo da ake ta gudanarwa
2019-09-23 10:36:26        cri
Kakakin gwamnatin yankin musamman na Hong Kong a jiya Lahadi da dare ya yi Allah wadai da ayyukan nuna karfin tuwo da barnata kayayyaki da masu tsattsauran ra'ayi suka yi ta gudanarwa a sassa da dama na yankin cikin kwanaki biyu da suka wuce.

Kakakin ya ce, a ranar Lahadi, masu zanga-zanga masu tsattsauran ra'ayi sun toshe hanyoyi a Shatin, inda suka cinna wuta da jefa bom da aka hada da gas. A sakamakon yadda suka lalata tashar jirgin kasa da ke Shatin, mazauna yankin sun kasa shiga jirgin. Ban da haka, sun kuma yi ta damun 'yan kasuwa da barnata na'urorin kasuwanni. Abubuwan da suka yi ba kawai sun saba wa doka ba, har ma ya keta hakkin mazauna yankin, tamkar aikin nuna son kai.

Baya ga haka, a ranar 22 ga wata, wasu masu zanga-zanga sun taru a tashoshin jirgi da suka hada da Tsing Yi, inda suka lalata na'urorin tashoshin. A wannan rana kuma, akwai wasu masu zanga-zanga masu tsattsauran ra'ayi da suka kafa shingaye da ma kunna wuta a dab da ofishin 'yan sanda da ke Mong Kok.

Kakakin ya ce, gwamnatin yankin musamman na Hong Kong tana Allah wadai da kakkausar murya da miyagun ayyukan da masu zanga-zangar suka aikata, kuma za a hukunta su bisa doka.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China