Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan sanda a Masar sun gano dan ta'addan da ya kaddamar da harin bam da wata mota
2019-08-09 10:11:17        cri
Wata sanarwar da ma'aikatar cikin gidan kasar Masar ta fitar a jiya Alhamis, ta ce rundunar 'yan sandan kasar ta samu nasarar gano mutumin da ake zargi, da kaddamar da harin bam da aka dana cikin wata mota a farkon makon nan a birnin Alkahira, wanda ya haddada rasuwar mutane 20.

Sanarwar ta bayyana Abdul Rahman Khaled Mahmoud, a matsayin wanda ake zargi, ta kuma ce mamba ne na kungiyar Hasm, mai alaka da kungiyar 'yan uwa musulmi da aka haramta a kasar. An dai tabbatar da hakan ne ta kwayoyin halittar mutumin, bayan gwada su da na wasu iyalan sa.

Ma'aikatar ta kuma ce, 'yan sanda sun gano maboya biyu ta 'yan ta'addan dake da hannu cikin kitsa wannan hari a lardin Fayoum, mai nisan kilomita 100 a kudu maso yammacin birnin alkahira, da kuma wani wurin dake birnin Shorouk mai makwaftaka da Alkahira.

Sanarwar ta tabbatar da cewa, an hallaka 'yan ta'adda 8 yayin musayar wuta a maboyar su dake Fayoum, kana aka harbe karin wasu 7 a birnin Shorouk, yayin artabu da 'yan sanda. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China