Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bukaci 'yan siyasan Amurka da kada su kulla kawance da 'yan a-ware na kasar Sin
2019-09-23 20:39:44        cri

A jiya Lahadi 22 ga watan nan ne sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo, ya ambato batun jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin, yayin da ya gana da ministocin harkokin waje na kasashe 5 na tsakiyar Asiya, yana mai cewa, matakan da kasar Sin take dauka a jihar ba shi da nasaba da yaki da 'yan ta'adda, ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su ki yarda da bukatar Sin ta dawowa da 'yan kabilar Uygur gida.

Dangane da kalaman nasa, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana yau a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing cewa, sakataren harkokin wajen Amurkan ya kaucewa gaskiya, ya kuma bata sunan kasar Sin dangane da manufarta kan jihar Xinjiang, kana ya tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin. Har ila yau abun da ya yi ya tona yadda Amurka ke nuna fuska biyu game da yaki da ta'addanci.

Ya ce kasar Sin ba ta ji dadin hakan ba, kuma tana adawa da hakan. Kaza lika kasar Sin ta bukaci Amurka, da ta dakatar da raba kafa kan yaki da 'yan ta'adda, da tsoma baki cikin batun jihar Xinjiang, da kuma goyon bayan masu bore na kungiyar East Turkistan, kada kuma ta zama abokiya ga kowane dan a-ware na kasar Sin, in ba haka ba, a karshe za ta illata moriyarta. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China