Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar harkokin wajen Sin ta kalubalanci Amurka da ta dakatar da matsawa wasu kamfanonin Sin lamba
2019-09-10 20:52:21        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Talata, cewa a cikin 'yan kwanakin da suka wuce, gwamnatin Amurka ta mayar kamfanin Huawei na kasar Sin na'urorin sadarwar da ta kwace shekaru biyu da suka wuce, matakin da Amurka ta dauka a hakika ya nuna cewa, ta amince da aikin da ta yi na sabawa dokoki. Kasar Sin ta kalubalanci kasar Amurka da ta dakatar da matsawa wasu kamfanoninta lamba.

Ban da wannan kuma, Hua Chunying ta nuna cewa, ya kamata kasar Amurka ta saurari ra'ayoyin da bangarori daban daban na kasarta ke fada, da kuma daina fakewa da batun kiyaye tsaro tana matsawa wasu kamfanonin kasar Sin, kana da samar wa kamfanonin Sin yanayin cinikayya da ya dace a Amurka. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China