Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bukaci Amurka da ta daina yin karya don bata sunan Sin
2019-09-24 19:53:44        cri

Yau Talata kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya kalubalanci kasar Amurka da ta daina kallon kasar Sin a matsayin mai hana bin addinai cikin 'yanci, ta kuma daina tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasar Sin bisa batun addini, kana ta daina yin karya don bata sunan kasar Sin.

Geng Shuang ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, inda ya kara da cewa, gwamnatin Sin tana tabbatar da bai wa al'umma 'yancin bin addinai bisa dokoki, kuma 'yan kabilu daban daban na kasar Sin suna bin addinai cikin 'yanci bisa dokoki. Amma kwanan baya, Amurka ta sha shafa wa kasar Sin kashin kaji, game da manufar tafiyar da harkokin jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta kasar a wurare da dama, da sunan addini da hakkin dan Adam, ta tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasar Sin.

Kasar Sin ta bayyana rashin amincewa da kalaman da abun da Amurka ta yi, ta kuma bukaci Amurka da ta soke tarurruka masu nasaba da wannan batu, ta dakatar da yin surutan banza kan batun Xinjiang, ta kuma dakatar da tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasar Sin bisa hujjar hakkin dan Adam. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China