Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta gamsu da takardun janye wasu kayayyaki daga jerin wadanda Amurka za ta kara kakabawa haraji
2019-09-25 11:19:58        cri

Kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin sun nuna cewa, Amurka ta gabatar da takardu 3, na janye wasu kayayyaki daga jerin wadanda za a kakabawa haraji a kwanakin baya, lamarin da ya shafi kayayyaki fiye da 400. Sin na goyon bayan kamfanonin da abin ya shafa, da su sayi wasu amfanin gona, ciki hadda wake daga Amurka bisa ka'idar kasuwa da tanade-tanaden WTO, kuma kwamiti mai kula da harkokin tsare-tsaren haraji na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, zai ci gaba da kawar da harajin da za a buga kan wadannan kayayyaki. Hukumomin dake da alaka da wannan batu sun bayyana cewa, Sin na da kasuwa mai girma, matakin dake nuna cewa, akwai makoma mai kyau wajen shigo da kayayyaki masu inganci daga Amurka, kuma Sin na sa ran bin hanya iri daya da kasar Amurka don samar da yanayi mai kyau ga hadin kansu a fannin aikin gona da sauran fannoni. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China