Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Li Keqiang ya gana da wakilan Amurka da suka halarci taron karawa juna sani tsakanin shugabannin kamfanonin kasashen biyu
2019-09-11 10:13:58        cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana da wakilan Amurka da suka halarci taron karawa juna sani tsakanin shugabannin kamfanonin Sin da Amurka da aka yi a jiya Talata a nan birnin Beijing.

Kungiyar 'yan kasuwa da masana'antu, da tawagar tsoffin manyan jami'an Amurka, sun ba da shawarwarinsu kan takaddamar ciniki dake tsakanin kasashen biyu. Kana Li Keqiang ya tattauna da su a yayin taron. Yayin wannan ganawa, Li Keqiang ya ce, shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 40 da kafuwar dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu. A cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, kasashen biyu sun rika samun bunkasuwa ta fuskar ciniki da tattalin arziki, inda suke neman amfanar juna da cin moriya tare. Ya ce kamata ya yi, kasashen biyu sun fidda wata hanya da ta dace, don magance bambancin ra'ayi tsakaninsu bisa ka'idar adalci da mutunta juna, karkashin matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma.

A nasu bangare, wakilan Amurka sun nuna cewa, shugabannin kamfanonin da suka halarci taron, sun dade suna shiga, da kuma ganewa idanunsu bunkasuwar dangantakar kasashen biyu, suna kuma kokarin gudanar da ayyukansu, da habaka zuba jari a kasar Sin, da neman hadin kai a dogon lokaci. Suna sa ran samun ci gaba cikin shawarwarin ciniki da tattalin arzikin tsakanin kasashen biyu, da kaiwa ga matsaya daya cikin sauri. Har ila yau sun yi imanin cewa, kasashen biyu na iya fidda wata hanya da ta dace, ta ingiza dangantakar kasashen biyu gaba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China