Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ba za ta janye karar Amurka da ta kaiwa WTO ba
2019-09-05 16:39:48        cri

Kwanan baya, Sin ta kai kara gaban kungiyar cinikayya ta duniya WTO, game da karin haraji da Amurka ta kakabawa kayayyakin da Sin din ke shigarwa Amurka, wadanda darajansu ta kai dala biliyan 300.

Game da hakan, mai magana da yawun ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin Gao Feng ya bayyana a yau Alhamis a nan birnin Beijing cewa, Sin ba za ta janye wannan kara ba.

Ban da wannan kuma, jami'an bangarorin biyu za su tattauna kan ajandar taron karawa juna sani tsakanin Sin da Amurka karo na 13, kan ciniki da tattalin arziki a birnin Washington a farkon watan Oktoba mai zuwa, don yin iyakacin kokari na samun ci gaba mai ma'ana tsakanin wakilan sassan biyu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China