Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaddamr da bikin nuna ci gaban bil Adamar Sin cikin shekaru 70 a Geneva
2019-09-10 10:39:54        cri

A jiya Litinin ne aka kaddamar da bikin nune-nune mai taken "Amfanawa jama'a: Ci gaban hakkin bil Adama da Sin take samu cikin shekaru 70 da kafuwarta" a Palace of Nations dake Geneva.

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD dake Geneva, kuma wakilin sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Switzeland Chen Xu, ya gabatar da jawabi a bikin budewa taron, inda ya ce, a cikin shekaru 70 da suka gabata, tattalin arziki da al'ummar kasar na samun bunkasuwa a dukkanin fannoni, kuma ana tafiyar da harkokin doka da shari'a yadda ya kamata.

Kazalika an kara kyautata hakkin wasu mutane na musamman, kamar tsoffi, da yara, da mata, da nakasassu da dai sauransu. Haka kuma Sin ta shiga ayyukan daidaita batun hakkin bil Adama na kasa da kasa, da sa kaimi ga raya kyakkyawar makomar al'ummar bil Adama baki daya.

Chen ya kara da cewa, Sin ta kan nacewa matsayin samun bunkasuwa, da gudanar da shari'a, da doka yadda ya kamata, da kara bude kofarta don tabbatar da hakkin bil Adam, bisa halin da kasar ke ciki da bukatun jama'arta.

Har ila yau, Sinawa za su hada kansu don bin hanyar tsarin mulkin gurguzu mai halayar musamman ta kasar Sin, karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar. Hakan ya sa, Sin za ta samun sabon ci gaba mai kyau ta fuskar hakkin bil Adama.

A nasu bangare kuwa, jakadun kasa da kasa suna sa ran koyi daga fasahohin kasar Sin, da fatan Sin za ta kara ba da shawarwarinta a wannan fanni, don gaggauta samun bunkasuwa a wannan fanni nan gaba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China