Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya jaddada muhimmancin kwarewar sana'o'i
2019-09-23 21:11:22        cri
Shugaban kasar Sin, kana babban sakataren kwamitin koli na JKS Xi Jinping ya bukaci matasan kasarsa da su maida hankali wajen kyautata kwarewarsu a fannin sana'o'i daban daban domin ciyar da kasa gaba.

Xi, wanda kuma shi ne babban jagoran kwamitin koli na rundunar sojojin kasar Sin, ya yi wannan kira ne cikin wani rubutaccen sako da ya aike ga Sinawa da suka shiga gasar kasa da kasa, ta gwada kwarewar sana'o'i karo na 45 da aka gudanar a birnin Kazan na kasar Rasha cikin watan da ya gabata.

A cikin sakon, shugaba Xi ya jaddada cewa, sana'o'in hannu na zama wani ginshiki na tallafawa samuwar hajoji kirar Sin, da wadanda ake kirkira a kasa, suna kuma taka rawar gani wajen samar da managarcin yanayin tattalin arziki.

Ya ce ya kamata a kara azama wajen kyautata tsarin samar da horo, da samar a ayyukan yi, da lura, tare da karfafa gwiwar masu sana'o'in hannu, da sauran sassa masu nasaba da hakan. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China