Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya aike da sakon taya murna ga taron masu kera kayayyaki na duniya na 2019
2019-09-20 14:18:40        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar taya murna ga taron masu kera kayayyaki na duniya da aka bude yau Juma'a a birnin Hefei dake lardin Anhui na gabashin kasar Sin.

Cikin wasikar, Xi Jinping ya ce, bangaren kera kayayyaki na duniya na fuskantar sauye-sauye, lamarin dake bukatar kasashe su kara kaimi ga hadin gwiwa da koyi da juna.

Shugaba Xi ya yi kira ga kasa da kasa, su yi amfani da damarmakin da sabon zagayen juyin juya halin kimiyya da ayyaukan masana'antu suka samar, su kara karfin kirkire-kirkiren fasaha a bangaren da samar da sauyi ta fuskar inganci da kwarin gwiwa.

Ya kara da cewa, a shirye Sin take ta yi aiki da dukkan bangarori wajen samar da sabbin fasahohi a bangaren da kuma ba da gudunmuwa ga ingantaccen ci gaba da samar da moriya ta bai daya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China