2019-09-20 19:48:03 cri |
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a kara azama, wajen fadada tsarin shawarwarin siyasa na Sin, karkashin majalissar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar ko CPPCC a takaice, tare da kara kyautata ayyukan majalissar ta fuskar ba da shawarwari, da sanya ido a fannin dimokaradiyya, da shigar kowa, tare da shiga a dama da kowa a harkokin kasa.
Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban hukumar zartaswa ta rundunar sojojin kasar, ya yi wannan kira ne a nan birnin Beijing, yayin taron karawa juna sani game da ayyukan majalissar ta CPPCC, wadda ke zuwa a gabar da majalissar ke cika shekaru 70 da kafuwa. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China