Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya mika gaisuwa ga manoma da ma maaikatan dake gudanar da ayyukan da suka shafi kauyuka da noma da kuma manoma
2019-09-23 11:27:06        cri

A yau Litinin ne aka shiga yanayin kaka da tsawon rana ke daidai da dare, a daya bangaren kuma, kasar Sin ke murnar ranar manoman kasar na samun girbi mai armashi karo na biyu, inda babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar kana shugaban kasar, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin kolin sojan kasar, Mr. Xi Jinping ya mika gaisuwar musamman ga manoma da ma ma'aikatan da suke gudanar da ayyukan da suka shafi kauyuka da noma da kuma manoma, tare da murnar fara aiki da kafar yada labaran noma da kauyuka ta gidan talabijin CCTV.

Tun a bara ne kasar Sin ta ware ranar shiga yanayin kaka da tsawon rana ke daidai da dare a kowace shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar a matsayin ranar da manoma ke murnar girbin amfanin gona mai armashi, rana ta farko da kasar ta ware musamman domin manoma. Kafar yada labaran noma da kauyuka ta CCTV ta kasance kafar musamman da kasar ta samar musamman domin yada labaran da suka shafi kauyuka da harkokin noma da manoma. A yau 23 ga wata ne, kafar ta fara aiki, inda a kowace rana, take watsa shirye-shiryen da suka kai tsawon sa'o'i 18. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China