2019-09-21 16:12:17 cri |
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi tir da harin da aka kai matatar man Saudiyya, yana mai kira da wadanda ke da hannu su kauracewa aiwatar da duk wani abu da ka iya ta'azzara zaman dar dar a yankin.
Shugaba Xi Jinping ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa ta wayar tarho da Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud a jiya Juma'a. Inda ya ce, yana fatan za a gudanar da cikakken bincike mai ma'ana da adalci kan hari, yana mai bukatar dukkan bangarori su hada hannu wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Shugaban na kasar Sin, ya kuma ce dangantakar kasarsa da Saudiyya ya samu ci gaba cikin sauri a shekarun baya-bayan nan, yana mai cewa kasashen biyu sun amfana sosai daga dangantakar, sannan kuma muhimman abokan hulda ne ga aikin gina Ziri Daya da Hanya Daya.
Ya ce kasar Sin na yabawa matakin Saudiyya na amincewa da manufar kasar Sin daya tak a duniya da kuma goyon bayan da take bayarwa game da batutuwan da ke da muhimmanci ga bukatu da muradun kasar Sin, yana mai cewa, ita ma kasar Sin, za ta tsaya tsayin daka, wajen goyon bayan kokarin Saudiyya na kare cikkaken ikonta da tabbatar da tsaro da zaman lafiya. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China