Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Somaliya ta katse huldar jakadanci da Guinea kan yankin Somali
2019-07-05 10:15:00        cri

Gwamnatin Somaliya ta sanar a jiya Alhamis cewa, ta katse huldar diflomasiyya da kasar Guinea, saboda yadda kasar dake yammacin Afirka ta keta 'yanci da hadin kan kasar ta Somaliya.

Ministan harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa na kasar Somaliya Ahmed Isse Awad, ya bayyana cewa, kasar Guinea ta baiwa shugaban yankin Somali Muse Buhi Abdi duk wata alfarma da ake baiwa shugaban kasa, lamarin da ya sabawa kudurorin MDD da na kungiyar tarayyar Afirka.

Yanzu haka dai shugaban yankin na Somali yana ziyara a Conakry bisa gayyatar shugaba Alpha Conde na Guinea.

Don haka Awad ya gargadi sauran kasashe da su guji keta 'yanci da hadin kan kasar Somaliya ta hanyar karfafa alaka da shugabannin yankin Somali.

A baya-bayan nan dai, yankin na Somali wanda ya ayyana 'yancin kansa daga Somaliya a shekarar 1991, ke ta kokarin neman kulla huldar jakadanci da wasu kasashe, domin neman samun amincewarsu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China