Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNHCR: 'Yan kasar Libya da suka rasa matsugunansu 10,500 ne suka samu tallafin jin kai tun barkewar fada a Tripoli
2019-09-02 11:16:25        cri
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD(UNHCR) ta bayyana cewa, 'yan kasar Libya 10,500 da suka rasa matsugunansu ne suka samu tallafin jin kai, tun lokacin da fada ya barke a ciki da wajen Tripoli, babban kasar Libya a watan Afrilu.

Tun a farkon watan Afrilu ne dai, gwamnatin Libya dake samun goyon bayan MDD ta fara kaddamar da mummunan hari a cikin da wajen Tripoli kan sojojin gwamnatin Khalifa Haftar dake da matsuguni a gabashin kasar, wadanda ke kokarin kwace birnin da ma hambarar da gwamnatin dake samun goyon bayan MDD.

Libya dai tana fadi tashin kafa gwamnatin farar hula ta riko, yayin da kasar ke fama da matsalar tsaro da rudani, tun bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar marigayi Muammar Gaddafi a shekarar 2011.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China