2019-08-02 10:35:51 cri |
Bayan zuba jarin dala miliyan 30, sabon kamfanin ya kuduri aniyar kera akwatin talabijin samfurin LED TV, kimanin 600,000, a kowace shekara, matakin da zai samar da guraben aikin yi sama da 600 ga mutanen Masar.
Kasar Masar tana da yawan jama'a, akwai kwanciyar hankali ta fuskar siyasa, kuma tana da ingantaccen muhallin zuba jari. Wadannan su ne dalilan da suka sanya kamfanin ya zabi kafa cibiyarsa a kasar, a cewar Zhou Chi, janar manajan kamfanin Konkan.
A zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Zhou ya ce, kamfanin Konka dake Masar zai samar da kayayyakinsa ga kasuwannnin Afrika, kuma kasar Masar wata muhimmiyar kasa ce wajen bunkasa cigaban gamayyar kasa da kasa karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya ta kasar Sin.
Shirin na hadin gwiwa ne, tsakanin kamfanin Konka da kamfanin samar da kayayyakin latironi na HOHO dake Masar. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China