Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sudan ya kafa kwamitin bincike kan rikicin ranar 3 ga watan Yuni
2019-09-22 15:44:50        cri
Firaministan Sudan Abdalla Hamdok, ya yanke shawarar kafa kwamiti mai zaman kansa, da zai yi bincike kan batun tarwatsa masu zanga-zangar da suka yi zaman dirshan a gaban hedkwatar rundunar sojin kasar, a ranar 3 ga watan Yuni.

Sanawar da majalisar ministocin kasar ta fitar a jiya, ta ce kwamitin ya kunshi mutane 7, ciki har da alkalin kotun koli da wakilai daga ma'aikatu daban daban, da kuma wasu lauyoyi 2 masu zaman kansu.

Bisa dokar kafa kwamitin bincike na 1954 ta kasar, kwamitin na da dukkan iko na gudanar da binciken da ya kamata.

Ana sa ran kwamitin ya kammala aikinsa cikin watanni 3, sannan ya na da damar tsawaita lokacin idan bukatar hakan ta taso.

A watan Augusta ne kwamitin mulkin soji na wucin gadi da kungiyar adawa, mai rajin tabbatar da sauyi da 'yanci, suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa mulkin hadin gwiwa na wucin gadi a kasar.

Bisa yarjejeniyar, za a kafa kwamiti mai zaman kansa da zai yi bincike kan rikicin da ya auku ranar 3 ga watan Yuni da sauran wasu rikice-rikice. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China