Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bukaci a goyi bayan gwamnatin Sudan wajen tabbatar da tsaro a Dafur
2019-08-27 09:59:14        cri
Mataimakin zaunannen wakilin Sin a MDD Wu Haitao, ya yi kira ga kasa da kasa, su taimakawa gwamnatin Sudan, wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na tabbatar da tsaro a yankin Dafur na kasar.

Wu Haitao, ya bayyanawa taron kwamitin sulhu na MDD kan shirin wanzar da zaman lafiya na hadin gwiwa tsakanin Majalisar da Tarayyar Afrika, wanda ke aiki a Dafur UNAMID cewa, ya kamata kasa da kasa su taimakawa gwamnatin Sudan wajen karfafa tsaro da shugabanci a Dafur, da kuma tabbatar da damka ayyukan tabbatar tsaron a hannun jam'an tsaron kasar cikin yanayin mafi dacewa.

Ya ce kasar Sin na goyon bayan janye shirin UNAMID da aka shirya yi a ranar 30 ga watan Yunin 2020, bisa kudurin kwamitin sulhun mai lamba 2429.

Ya kuma bukaci a sake fara aiwatar da tsare-tsaren wanzar da zaman lafiya a Dafur tun da wuri. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China