Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar mamakon ruwan sama da ambaliya a Sudan ya karu zuwa 62
2019-08-26 13:44:05        cri

Ma'aikatar lafiya ta kasar Sudan, ta ce adadin wadanda suka mutu sanadiyyar mamakon ruwan sama da ambaliya a kasar, ya karu zuwa 62.

Yayin wani taron manema labarai a birnin Khartoum, babban birnin kasar, mukaddashin mataimakin ministan lafiya, Sulaiman Abdul-Jabbar, ya ce adadin wadanda iftila'in ya yi sanadin mutuwarsu ya kai 62, yayin da wadanda suka jikkata ya kai 98.

Ya ce jimilar iyalai 35,850 ne iftila'in ya shafa a fadin kasar, yana mai cewa ya kuma lalata gidaje 22,676 baki daya, yayin wani bangare na gidaje 13,074 ya lalace. Baya ga haka, dabbobi 3,636 sun mutu.

Sai dai, Sulaiman Abdul-Jabbar ya ce kasar tana da karfin tunkarar hadarruran na lokacin da ake ciki na damina. Kuma ba a kai matakin ayyana iftila'i ko neman taimakon kasashen waje ba.

Tun daga farkon watan Augusta, galibin jihohin kasar ke fama da mamakon ruwan sama da ya yi sanadin lalata gidaje da tituna. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China