Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IGAD ta yi maraba da ganawar sassan Sudan ta Kudu
2019-09-11 10:50:27        cri
Kungiyar kasashen gabashin Afirka ta IGAD, ta jinjinawa ganawar da tsagin shugaban gwamnatin Sudan ta kudu Salva Kiir Mayardit ya yi, da jagoran 'yan adawar kasar Riek Machar a birnin Juba fadar mulkin kasar.

Mr. Machar, wanda ke jagorantar gungun 'yan adawar kasar ko SPLM-IO, wanda aka yiwa daurin talala tun a shekarar 2016, ya koma Sudan ta kudu a ranar Litinin, bisa rakiyar mataimakin shugaban kwamitin soji mai rikon kwarya a kasar Sudan Mohamed Hamdan Daqlu, da kuma wasu karin jami'ai 70.

Cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Talata, kungiyar IGAD ta yi maraba da ganawar shugaba Salva Kiir Mayardit da jagoran 'yan adawa Riek Machar. Sanarwar ta ce, hakan zai ba da damar warware sauran batutuwa dake kawo tarnaki ga tsaron kasar, da batun shata kan iyakokinta, da yawan jihohi da sauran su.

Sanarwar ta kara da cewa, ganawar sassan biyu ta zo kan gabar da ake bukatar ta, kasancewar baya ga yiwuwar kawo karshen kalubalen mika mulki da za ta iya haifarwa, a hannu guda kuma, za ta taimaka wajen gina imani da juna tsakanin sassan da a baya ba sa ga maciji da juna, ta kuma farfado da aiwatar da yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya a kasar, wadda tashe tashen hankula suka daidaita. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China