Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sudan yayi fatali da masu yin shisshigi a zaben ministocin gwamnatin rikon kwarya
2019-09-02 11:10:08        cri
Firaministan Sudan Abdalla Hamdok, ya jaddada aniyarsa ta yin watsi da duk wani yunkurin yin katsa landan wajen zaben ministoci a gwamnatin rikon kwaryar kasar.

Hamdok ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa, inda ya kalubalanci jam'iyyar adawa ta Freedom and Change Alliance kan jerin adadin wadanda za a nada da ta gabatar.

Ya jaddada aniyar bin tsarin cancanta wajen zabar ministocin, wanda haka ne kadai zai taimaka wajen dora kasar kan tudun mun tsira.

Ya kara da cewa, kawo yanzu sunayen mutane 7 ne aka zaba daga cikin wadanda ake son nadawa a mukamin ministocin, inda ya bukaci gamayyar 'yan adawar dasu lalibo wasu hanyoyi masu bullewa cikin sa'o'i 24.

A ranar 28 ga watan Agusta, Hamdok ya shirya kafa majalisar ministoci wanda gamayyar 'yan adawar Freedom and Change Alliance zasu gabatar da sunayen, in banda ministocin tsaro da na harkokin cikin gida wadanda majalisar sojoji kasar zata zaba.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China