Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sudan ya karbi jerin sunayen wadanda ake son nadawa Ministoci
2019-08-28 10:17:31        cri
Firaministan Sudan Abadalla Hamdok, ya karbi jerin sunayen wadanda ake son nadawa ministoci a gwamnatin riko.

Abdallah Hamdok, ya yi alkawarin yin cikakken nazari kan dukkan wadanda aka zabo bisa mizanin da aka amince da shi, domin bada wakilcin da ya dace ga mata.

A yau Laraba 28 ga wata, Abadalla Hamdok zai kafa majalisar ministoci, wadanda kungiyar kawance ta Freedom and Change alliance ta zabo, in banda ministan tsaro da na harkokin cikin gida, da sojoji mambobin kwamitin ikon kasar za su zaba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China