Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kira taron wanzar da zaman lafiya cikin Afghanistan a Qatar
2019-07-08 13:44:12        cri

Qatar da Jamus sun hada kai wajen gudanar da taron wanzar da zaman lafiya cikin gidan Afghanistan a birnin Doha, fadar mulkin Qatar, a jiya Lahadi. Wakilai fiya da 60 daga gwamnati da darikoki daban-daban na Afghanistan, a matsayin daidaikun mutane, sun halarci taron na kwanaki biyu.

Wakilan Qatar da Jamus sun nuna cewa, taron ya kasance hakikanin matakin da Afghanistan ke dauka don cimma burin jama'arta na ci gaba da yin tattaunawa don samun zaman lafiya, matakin da zai taimakawa darikoki mahalartan taro da su amince da juna da samarwa musu wata hanya da ta dace don yin tattaunawa tsakaninsu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China