Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane miliyan 1.3 na bukatar agajin jin kai a yankunan Kamaru dake da rinjayen masu amfani da turancin Ingilishi
2019-07-23 10:26:38        cri

MDD ta ce yanayin jin kai a arewa maso yammaci da kudu maso yammacin Kamaru na ci gaba da tabarbarewa, inda ake da mutane miliyan 1.3 dake bukatar taimako.

Mataimakin kakakin Sakatare Janar na MDD Farhan Haq, ya ce mutane 530,000 ne ke gudun hijira a wadancan yankunan biyu, sannan an tilastawa mutane kusan 40,000 tserewa zuwa Nijeriya.

Ya ce yanayin na tabarbarewa ne saboda ci gaba da keta hakkokin bil Adama da rashin kariya, yana mai cewa a cikin watanni 6 na bana, an samu rahoton take hakkokin bil Adama sama da 2,800.

Duk da karuwar bukatar agaji, aikin agajin jin kai a Kamaru, na zaman daya daga cikin wadanda ke fuskantar matsanancin rashin kudi a duniya.

Masu aikin agaji sun bukaci dala miliyan 300, amma kaso 20 cikin 100 na kudin kawai aka samu a bana. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China