Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Kamaru ya karyata zargin tarkon bashi da wasu ke dangantawa da kasar Sin
2019-08-08 15:30:53        cri

Firaministan kasar Kamaru Joseph Dion Ngute, ya karyata zargin da wasu kafafen yada labaran yammacin duniya ke yadawa na danganta kasar Sin da dana tarkon bashi.

Kamaru kasa ce mai ikon gashin kanta, harkokinta ba al'amari ne da ya shafi wani ba. Muna iya gudanar da hakikanin abin da muke so domin bunkasa kasarmu, a cewar Ngute, a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, a lokacin da ya kai ziyarar duba wurin gina wani masana'antar samar da ruwa wanda wani kamfanin kasar Sin ke daukar nauyin gudanarwa.

Aikin wanda ke gudana a yankin Yaounde babban birnin kasar, wanda aka kaddamar a karshen shekarar 2016 kana ake sa ran kammalawa a karshen wannan shekarar ta 2019.

Idan aikin ya kammala, masana'antar za ta dinga samar da ruwa kimanin cubic mita 300,000 a ko wace rana, za ta biya bukatun mutane miliyan 2 da rabi a babban birnin kasar da wuraren da ke kewayensa.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China