Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan ta Kudu ta mai da hankali sosai kan bikin baje kolin cinikayya tsakani Sin da Afrika
2019-06-06 13:36:52        cri
Shugabannin gwamnati da kamfanonin Sudan ta Kudu suna shirin shiga bikin baje kolin cinikayya tsakanin Sin da Afrika karo na farko, da zummar jawo hankalin masu zuba jari ga kasar, wadda ta kasance kasa mafi karancin shekaru a nahiyar.

Kakakin ministan harkokin waje na kasar Mawien Makol Ariik ya shedawa manema labarai cewa, shugaban kasar na farin ciki kwarai da gaske don shiga wannan biki tare da sauran abokan kasashe 52 na nahiyar, wanda aka shirya gudanar da shi daga ranar 27 zuwa 29 ga watan Yuni a lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin. Ya kara da cewa, dukkanin kasashen gabashin Afrika, wadanda suke mallakar man fetur masu dimbin yawa za su halarci bikin don kafa sabon tsarin ciniki tare da kasar Sin.

Ya ce, bikin ya kasance wani dandali ne mai kyau ga kasarsa don samun wata damar bayyanawa sauran kasashe kokarin da Sudan ta Kudu take yi na tabbatar da zaman lafiya da karko mai dorewa, a sanadin haka, kasar ta zama wuri mai kyau da za a zuba jari da kulla dangantakar cinikayya.

Wannan biki da za a gudanar a birnin Changsha, hedkwatar lardin Hunan, zai samu halartar baki har 1500, da Sinawa fiye da 5000, da 'yan kasuwa 3500. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China