![]() |
|
2019-06-21 10:29:41 cri |
An wallafa littafi mai taken "Sin da Rwanda", da shahararren Dan Jaridan kasar Rwanda Gerald Mbanda ya rubuta, jiya Alhamis, a Kigali, fadar mulkin kasar. Gerald Mbanda ya bayyana yadda karfin shugabanci ya taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga matakin sauya hanyar bunkasuwar kasar da Sin da Rwanda suka gudanar, bisa fannoni uku, wato tarihi, siyasa da tattalin arziki. A ganinsa, kasashen biyu sun samu irin wannan ci gaba ne sakamakon karfin yin kwaskwarima da kuma karfin shugabanci mai inganci da Xi Jinping da Paul Kagame suke da su a cikin jam'iyyunsu. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China