Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar maaikatan jinyya zagaye na 29 mai taimakawa kasar Equatorial Guinea ta samu lambar yabo ta koli a kasar
2019-07-16 10:52:41        cri

Kwamitin kiwon lafiya na lardin Guangdong na kasar Sin ya ba da labari a jiya Litinin cewa, gwamnatin Equatorial Guinea ta baiwa tawagar ma'aikatan jinyya zagaye na 29 mai taimakawa kasar lambar yabo ta koli wato lambar yabo mai daukaka ta 'yancin kan kasar, don yabawa gudummawar da ta bayar a cikin wa'adinsa na shekara daya da rabi da suka gabata.

An ce, tun shekaru 70 na karni na 20, lardin Guangdong ke zabar kwararrunsa ta fuskar jinyya yana turawa zuwa kasashen Afrika don gudanar da aikin jinyya. Wannan tawaga ta tashi daga kasar Sin a ranar 5 ga watan Jarairu na shekarar 2018 don gudanar da aikinta na wa'adin shekara daya da rabi a kasar Equatorial Guinea.

A cikin wadannan shekara daya da rabi, tawagar ta yi jinyyar mutane 7689, da yin tiyata sau 1349 kana da ceton mutane masu rashin lafiya mai tsanani 116 da yin allurar gargajiya ta kasar Sin ga mutane 1420. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China