Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kashe 'yan bindiga 8 tare da jikkata 12 a kudancin Somaliya
2019-07-01 09:50:11        cri
Rahotanji daga kasar Somaliya na cewa, dakarun kasar sun yi nasarar kashe 'yan bindiga 8 tare da jikkata wasu 12, a wani dauki ba dadi tsakanin dakarun gwamnati da masu tsananin kishin addini na al-Shabab a kauyen Moro Gabey mai nisan kilomita 30 daga garin Hudur a yankin Bakol dake kudancin kasar ta Somaliya.

Kwamishinan garin Hudur Mohamed Mo'alim Ahmed ya shaidawa manema labarai cewa, fadan ya barke ne bayan da dakarun gwamnati suka kaddamar da hari kan mayakan dake karbar haraji da karfi daga wajen mazauna kauyen Moro Gabey.

Wannan mataki na zuwa ne, bayan da dakarun gwamnati a ranar Alhamis din da ta gabata suka kashe mayakan al-Shabab 8, a wani hari da suka kaddamar a garin Jamame na yankin Lower Juba dake kudancin kasar.

Dakarun Somaliya dai sun zafafa kai hare-hare kan kungiyar dake da alaka da al-Qaida a yankunan tsakiya da kudancin kasar da nufin fatattakar 'yan tawayen daga wadannan yankuna.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China