Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ta kakabawa hukumar zirga-zirgar sama ta Iran takunkumi
2019-09-04 20:40:21        cri

Ma'aikatar kudi ta Amurka, ta saka takunkumi kan hukumar sararin sama da sauran wasu sassan nazari biyu dake karkashinta bisa dalilin cewa, wai na'urar da take kerawa na iya harba makamai masu linzami.

Sakataren harkokin waje na kasar Amurka Mike Pompeo ya ce, a karo na farko, Amurka ta kakabawa hukumar takunkumi, bisa zargin fitar da na'urar harba makamai masu linzami. Bisa tanadin tsarin Amurka, za a daskarar da kadarorinta dake Amurka, kuma 'yan kasar Amurka ba za su iya yin ciniki da hukumar ba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China