Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iran ta bukaci bin hanyoyin diflomasiyya game da takaddamarta da Amurka
2019-08-26 14:01:23        cri

Ministan harkokin wajen kasar Iran, Javad Zarif, ya bayyana matsayar Iran ta warware sabaninta da Amurka ta hanyoyin diflomasiyya.

Javad Zarif ya bayyana haka ne a shafinsa na Tweeter, bayan ziyarar ba-zata da ya kai jiya Lahadi, zuwa garin Biarritz na kasar Faransa, inda ake gudanar da taron kasashen G7 karo na 45.

Bayan ganawarsa da shugaban Faransa, Emmanuel Macron da takwaransa na Faransar Jean-Yves Le Drian, a gefen taron na G7 domin tattauna hanyoyin rage tankiyar da ake tsakanin Amurka da Iran, Javad Zarif ya wallafa a shafin Tweeter cewa, Iran za ta ci gaba da bin hanyoyin diflomasiyya domin cimma yarjejeniya mai ma'ana.

Ya ce abun da ake tunkara a gaba na da wuya, amma ya cancanci gwaji. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China