Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Iran: Sharadin yin shawarwari da Amurka shi ne Amurka ta koma yarjejeniyar nukiliyar Iran
2019-08-28 14:04:16        cri

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya bayyana a jiya Talata cewa, sharadin farfado da shawarwari tsakanin Iran da Amurka shi ne, Amurka ta koma yarjejeniyar nukilyar Iran, yana mai cewa babu wata hanya ta daban da ta wuce gudanar da shawarwari karkashin yarjejeniyar.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Iran na IRNA ya ruwaito shugaban na cewa, Amurka ita ce ke rike da mabudin magance wannan batu. Idan ba ta soke takunkumin da ta kakabawa kasar Iran ba, dangantakar kasashen biyu za ta yi tafiyar hawainiya.

Shugaba Rouhani ya kuma ce, Iran ba ta son yin gaba da kowace kasa, hadin kai da sauran kasashe take sa rai.

An ba da labarin cewa, yayin taron koli na G7 da aka gudanar a Faransa a ran 26 ga wata, shugaba Donald Trump na Amurka ya ce, idan aka gabatar da sharadi mai dacewa, zai yi shirin daukar shawarar da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gabatar na yin shawarwari da shugaba Hassan Rouhani.(Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China