Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump ya ce a shirye yake ya tattauna da shugaban Iran bisa shawarar Faransa
2019-08-27 10:59:07        cri

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce a shirye yake ya tattauna da takwaransa na Iran, Hassan Rouhani, idan akwai bukatar hakan.

Donald Trump ya bayyanawa wani taron manema labarai da ya yi tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron, a karshen taron kungiyar G7 a birnin Biarritz na Faransa cewa, kafin lokacin tattaunawar, ya kamata Iran ta yi taka tsantsa.

Shugaba Emmanuel Macron ne ya bada shawarar gudanar da tattaunawar, inda ya ce shi ma shugaban Iran, a shirye yake ya tattauna da Trump.

Da yake kara sukar yarjejeniyar da aka cimma a Tehran a 2015, shugaba Trump ya ce, kungiyar G7 na aiki kan wata yarjejeniya mai dogon zango da za ta tabbatar da Iran bata mallaki makaman nukiliya ko masu linzami ba.

Ya kara da cewa, yana ganin shugaban Iran zai so su gana. Kuma Iran na son daidaita takkadamar, domin suna dandana kudarsu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China