Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin ya bukaci kasashen duniya da su tallafawa Libya magance kalubalen siyasa
2019-09-05 19:44:25        cri
Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya yi kira ga kasashen duniya da su dauki sahihan matakan tallafawa kasar Libya, ta yadda za ta samu zarafin ci gaba da tattaunawar siyasar.

Wu Haitao ya ce cikin shekaru 8 da suka gabata, Libya ta kasance cikin wani mawuyacin hali, inda al'ummar take shan fama da tashe-tashen hankula, yayin da yanayin tsaro da na jin kai a sassan dake kewayenta ke kara tabarbarewa.

Wu Haitao, ya bayyana hakan ne yayin da yake karin haske, game da halin da ake ciki a Libya, lokacin zaman kwamitin tsaron MDD da ya gudana a jiya Laraba.

Daga nan sai jami'in ya sake jan hankalin kasashen duniya, da su taka rawar gani, wajen zakulo hanyoyin kawo karshen tarbarwar dake wakana a Libyan. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China