Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu kamfanonin kasar Sin sun fara sayen amfanin gona daga Amurka
2019-07-22 11:39:20        cri
Rahotanni sun bayyana cewa, Sin da Amurka na tabbatar da aiwatar da wasu muhimman ra'ayoyin da shugabanninsu suka cimma tare a wajen taron kolin G20 da aka yi kwanakin baya a birnin Osakar kasar Japan a halin yanzu. Haka kuma Amurka ta sanar da soke harajin da ta sanyawa wasu kayan masana'antu da ire-irensu suka kai 110 da kasar Sin ta fitar zuwa kasar, ta kuma bayyana fatanta na taimakawa kamfanonin Amurka ci gaba da samar da hajoji ga kasar Sin. A halin yanzu, akwai wasu kamfanonin kasar Sin wadanda suka fara tambayar farashin amfanin gona daga 'yan kasuwar Amurka, da neman samun izinin dakatar da kara buga haraji kan amfanin gonar da za su saya daga Amurka bisa ka'idojin kwamitin tsara ka'idojin buga haraji na majalisar gudanarwa ta kasar. Shi kuma kwamitin zai tantance bukatar wadannan kamfanonin na kasar Sin.

Domin biyan bukatun masu sayayya na kasar Sin, akwai wasu kamfanonin kasar wadanda ke da niyyar ci gaba da shigowa da wasu amfanin gona daga kasar Amurka. Hukumomin Sin sun ce, suna fatan Amurka za ta hada kai tare da Sin domin cika alkawarin da ta dauka.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China