![]() |
|
2019-06-20 20:47:01 cri |
Rahotanni sun ruwaito cewa, dan majalisar dattawan kasar Amurka Marco Rubio, ya gabatar da wani daftarin doka, inda ya nemi a yi gyaran fuska ga dokar mika ikon tsaron kasar Amurka, wato NDAA, ta yadda za'a hana kamfanin Huawei, da sauran wasu kamfanonin kasar Sin su nemi tallafi bisa dokar kare 'yancin mallakar fasaha ta Amurka, kuma a hana su gabatar da kara ta fannin kare 'yancinsu na mallakar fasaha, al'amarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kasar ta Amurka.
Game da wannan batu, Lu Kang ya jaddada cewa, Sin ta nemi Amurka da ta gaggauta dakatar da aikata laifi, kana za ta ci gaba da daukar duk wani matakin da ya wajaba, don kare hakkokin kamfanonin kasar.(Murtala Zhang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China