Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Amurka za su dawo da tattaunawar cinikayya bisa tushen nuna daidaito da mutunta da juna
2019-07-11 20:08:50        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin Gao Feng ya bayyana cewa, kasashen Sin da Amurka, za su dawo da tattaunawar cinikayya a tsakanisu bisa tushen nuna daidaito da mutunta juna, inda ake fatan sassan biyu za su kai ga warware muhimman fannoni da suke takaddama a kai.

Gao wanda ya bayyana hakan Alhamis din nan yayin taron manema labaran da aka saba gudanarwa, ya ce kasashen biyu, za su kai ga warware banbance-banbancen cinikayyar dake tsakaninsu ta hanyar mutunta bukatun juna ta hanyar tattaunawa.

A ranar Talata ce kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, gwamnatin Amurka ta ce, za ta fitar da wasu kayayyakin kasar Sin, wadanda suka hada da kayayyakin kiwon lafiya da wasu muhimman na'urori, daga harajin kaso 25 cikin 100 da tun farko ta ce za ta kakabawa kayayyakin kasar ta Sin dake shiga Amurka, bayan da wasu kamfanonin Amurka suka yi korafi game da karin harajin.

Jami'in na kasar Sin ya bukaci Amurka, da ta cika alkawarinta ta kuma daina nuna son kai da neman gurgunta kamfanonin kasar Sin, yana mai cewa, wasu kamfanoni kamar Huawei, har yanzu na cikin jerin kamfanonin da Amurka ke neman hana su shigo da kayayyakin su cikin kasarta.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China