Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakataren harkokin wajen Amurka ya kai ziyarar ba-zata Afghanistan
2019-06-26 10:41:47        cri
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya kai ziyarar ba-zata birnin Kabul na kasar Afghanistan jiya Talata, inda ya yi shawarwari da wasu shugabannin kasar game da batun gudanar da tattaunawar shimfida zaman lafiya.

Rahotanni daga gidan talabijin na kasar Afghanistan sun ce, Pompeo ya ziyarci Afghanistan ba tare da ya sanar ba. Bayan ganawarsa da shugaban Afghanistan Ashraf Ghani gami da babban jami'in gudanarwa na gwamnatin kasar Abdullah Abdullah, Mike Pompeo ya bayyanawa 'yan jaridu cewa, shi da shugabannin biyu na Afghanistan, sun cimma matsaya daya kan cewa, zaman lafiya na gaba da komai, kuma Afghanistan ba za ta yarda da duk wani aikin ta'addanci da ya wakana a kasar ba.

Kuma bisa sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar, Pompeo ya nuna cewa, Amurka da Taliban sun samu babban ci gaba wajen gudanar da shawarwarin yaki da ta'addanci, inda ake sa ran cimma yarjejeniyar shimfida zaman lafiya kafin ranar 1 ga watan Satumbar bana.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China