Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Sudan ta kudu ta amince ta jinkirta kafa gwamnatin hadin kan kasa
2019-05-08 10:04:48        cri
Ministan watsa labarai da sadarwa na kasar Sudan ta kudu Micheal Makuei Lueth, ya bayyana cewa, gwamnati ta amince ta kara wa'adin kafa gwamnatin hadin kasa zuwa watanni shida, a wani mataki na hana sake fadawa yakin basasa.

Makuei ya bayyana cewa, da farko gwamnatin Salva Kiir ta ki amincewa a jinkirta kafa gwamnatin hadin kasa fiye da wa'adin farko na ranar 12 ga watan Mayun wannan shekara, amma yanzu ta goyi bayan wannan mataki saboda zaman lafiya.

Jami'in ya ce, gwamnati ba ta goyon bayan sake komawa gidan jiya, sannan ba ta son a ce yarjejeniyar ta rushe, burinsu shi ne kafa gwamnatin da kowa zai amince da ita. A don haka suka goyi bayan kara wa'adin kafa gwamnatin hadakar. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China