Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta ci gaba da tallafawa shirin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta kudu
2019-05-09 09:31:45        cri
A jiya Laraba jakadan kasar Sin ya bayyana cewa kasarsa za ta ci gaban ba da taimako domin tabbatar da samun dauwamamen zaman lafiya a Sudan ta kudu.

Hua Ning, jakadan kasar Sin a Sudan ta kudu, ya bayyana hakan ne a Beijing a lokacin da yake bayyana irin muhimman matakai da bangarori daban daban suka dauka tare da tallafin hukumomin shiyyar gabashin Afrika, da kungiyar raya ci gaban kasashen gabashin Afrika (IGAD), tare da hadin gwiwar al'ummomin kasashen duniya, wadanda ke kokarin samar da kyakkyawan sakamako wajen cimma nasarar samar da dauwamammen zaman lafiya.

Jakadan ya bukaci al'ummomin kasashen duniya da masu ruwa da tsaki da su samar da taimako don samun dauwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a jaririyar kasar, yana mai cewa, gwamnatin Sin za ta ci gaba da bada dukkan taimakon da ya dace wanda zai taimakawa shirin wanzar da zaman lafiya a kasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China