Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Kenya a Sudan ta kudu yana kokarin ganin an aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya
2019-08-09 10:50:30        cri
Jakadan musamman na kasar Kenya a Sudan ta kudu, Kalonzo Musyoka, ya isa Juba, babban birnin kasar a ranar Alhamis, domin bibiyar yadda za'a aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar kasar wacce aka cimma matsaya kanta a watan Satumbar shekarar 2018.

Fadar shugaban kasar Sudan ta kudun ta sanar da cewa, Musyoka ya gana da shugaban kasar Salva Kiir, da sauran manyan jami'an gwamnatin kasar domin tattaunawa game da irin nasarorin da aka samu a yarjejeniyar zaman lafiyar.

Wakilin na Kenya zai kuma gana da bangarorin masu ruwa da tsaki domin neman amincewarsu da su goyi bayan kafa gwamnatin wucin gadi ta hadin kan kasa nan da ranar 12 ga watan Nuwamba.

Sanarwar da ofishin shugaban kasar Kiir ta fitar tace, an shirya taron tuntubar da masu ruwa da tsaki da bangarori masu sanya hannu kan yarjejeniyar farfado da zaman lafiyar kasar da nufin samun nasara wajen kammmla dukkan shirye shiryen da suka dace na kafa gwamnatin wucin gadi ta hadin kai nan da ranar 12 ga watan Nuwambar 2019. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China