Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Sudan ta kudu ya bukaci a aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya kasar cikin lumana
2019-05-16 10:13:48        cri
Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir, ya bukaci kungiyoyin 'yan adawar kasar da su ajiye dukkan banbance-banbancen dake tsakaninsu kuma su hada gwiwa da gwamnati domin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar kasar yadda ya kamata.

Kiir, ya kuma bukaci 'yan adawar da su ja kunnen magoya bayansu da su guji shiga zanga-zangar da ake tsammanin shiryawa gabanin bikin tunawa da ranar sojojin kasar wanda aka shirya gudanarwa a yau Alhamis.

Shugaba Kiir ya kara da cewa, mummunan tashin hankalin kasar ba zai taba karewa ba muddin muka ci gaba da yin abubuwan da aka saba yi a baya. Aiwatar da sabuwar yarjejeniyar zaman lafiyar cikin nasara zai share fagen samun nasarar shirya zabe ta hanyar demokaradiyya a kasar a matsayin wani tushen da zai bada damar gina dawwamamman zaman lafiya a kasar.

Kiir ya bayyana a Juba cewa, "Ya kamata mu ajiye kwadayin son mulki a gefe, mu mayar da hankali kan zaman lafiyar kasarmu kuma mu mayar da kasar kan turbar mulkin demokaradiyya kuma mu baiwa jama'a damar yin rayuwa a duk inda ya dace."

Shugaban kasar, wanda ya gabatar da jawabin yanayin da kasar ke ciki gabanin bikin tunawa da cika shekaru 36 da kafuwar rundunar sojojin 'yantar da al'ummar Sudan (SPLA/M) wanda ta sanadinta ne aka samu 'yancin kasar. Ya ce da yawa daga 'yan kasarsa sun kauce daga kan manufar fafutukar wanda aka kafa da nufin tabbatar da tsarin mulkin demokaradiyya da gina makomar kasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China