Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bai dace a fake da Sin a halasta ficewar Amurka daga yarjejeniyar INF ba in ji wakilin Sin
2019-08-23 10:56:12        cri
Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya ce sam bai dace Amurka ta fake da kasar Sin, ta halastawa kan ta ficewa daga yarjejeniyar dakile matsakaitan makaman nukiliya ta INF ba.

Zhang wanda ya bayyana hakan, yayin zaman gaggawa na kwamitin tsaron MDD da ya gudana a jiya Alhamis mai taken "barazana ga tsaro da zaman lafiyar kasa da kasa", ya ce har kullum Sin na amfani da manufofin ta na tsaro ne domin kare kai. Kaza lika manufarta ta mallakar nukiliya na da alaka ta kai tsaye da tsaron kasa, tana kuma gudanar da hakan ba tare da wata rufa rufa ba.

Ya ce a tsawon shekaru, Sin na shiga ayyukan dakile yaduwar makamai, da shawarwari da musayar ra'ayoyi, karkashin tsarin cudanyar sassa daban daban, wadanda suka hada da na MDD mai nasaba da shirin kwance damara.

A hannu guda kuma, Sin na adawa da takarar mallakar makamai, tana kuma aiki tukuru wajen samar da daidaito, da kariya ga tsaron kasa da kasa.

To sai dai kuma a cewar jami'in na Sin, ficewar Amurka daga waccan yarjejeniya, ta haifar da durkushewar yarjejeniyar, matakin da ka iya yin mummunan tasiri ga tsaro, da daidaito a matakin kasa da kasa, da ma tsaron shiyyoyin Turai da Asiya. Kaza lika zai iya yin tasiri ga kudurin kasashen duniya na dakile yaduwar makamai.

Daga nan sai ya yi kira ga kasashen duniya, da su maida hankali kan wannan lamari.

Ficewar Amurka daga INF dai ta kawo karshen yarjejeniyar a ranar 2 ga watan Agusta. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China