Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da taron kara juna sani game da kimiyyar Telebijin na kasa da kasa na shekarar 2019 a Beijing
2019-05-23 16:58:59        cri

Babban gidan rediyo da Telebijin na kasar Sin (CMG) ya dauki bakuncin gudanar da taron kimiyyar Telebijin na kasa da kasa na shekarar 2019. Taron da ya samu halartar kwararru fiye da 500 daga fannonin kafofin yada labarai, sadarwa, kimiyyar watsa labarai da dai sauransu.

Yayin bikin bude taron, cibiyar kula da fasaha na CCTV karkashin rukunin CMG ta kulla wata yarjejeniyar hadin kai da jami'ar nazarin harkokin sufuri ta birnin Shanghai, don gina wani dakin gwajin fasahohin telebijin na zamani.

Wani jami'in CMG ya nuna cewa, ana cikin zamanin fasahar 5G, ya kamata mu yi amfani da wannan zarafi mai kyau don bullo da wani tsari mai kyau na kimiyyar Telebijin wato "5G+4K+AI", ta yadda za a gaggauta yin amfani da kimiyya da fasahohi daban-daban a wannan fanni. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China