Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CMG ya shirya bukukuwa a dandalin tattaunawar tattalin arzikin Saint Petersburg
2019-06-07 19:41:02        cri

Yau Jumma'a babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG a takaice, ya daddale yarjejeniyar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, da asusun shirya baje kolin kasar Rasha a Saint Peterburg na Rasha, inda aka gudanar da taron kaddamar da watsa gajerun hotunon bidiyo a jere, wadanda aka tsara kan batutuwa game da biranen sada zumunta dake tsakanin Sin da Rasha.

Bisa yarjejeniyar da sassan biyu suka daddale, kafofin watsa labarai na kasashen Sin da Rasha, za su kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu bisa ka'idar daidai wa daida, da moriyar juna, da bude kofa ga juna karkashin jagorancin tsarin dandalin tattaunawar tattalin arzikin Saint Petersburg, da tsarin dandalin tattaunawar tattalin arzikin kasashen gabashin duniya. Kana sassan biyu za su kara karfafa cudanyar watsa labarai dake tsakaninsu, ta yadda za su samar da karin bayanai na gaske ga masu sauraro, da 'yan kallo na kasashen nan biyu.

Shugaban CMG Shen Haixiong ya bayyana cewa, yanzu haka huldar dake tsakanin Sin da Rasha ta shiga wani sabon matsayi a sabon zamanin da ake ciki, a don haka ya dace kafofin watsa labarai na sassan biyu su kara gudanar da hadin gwiwa dake tsakaninsu, domin kara taka rawa wajen bayyana ra'ayin jama'a a fadin duniya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China