![]() |
|
2019-08-21 09:32:08 cri |
Wata sanarwar da ECA ta fitar, ta ruwaito Shugaban cibiyar kula da tsarin cinikayya na nahiyar Afrika ta hukumar, David Luke na cewa, bai kamata Ghana ta tsaya ga aiwatar da tsarin yankin wajen inganta samun ci gaba cikin dogon zango ba kadai, yana mai cewa, kamata ya yi ta kuma tabbatar da fadada cin gajiyar ci gaba domin rage fatara da inganta zaman rayuwar al'ummar kasar baki daya.
Ghana na daga cikin kasashe na farko da suka amince da yarjejeniyar kafa yankin a hukumance cikin watan Mayun bara, bayan ta sanya hannu kan yarjejeniyar a lokacin da aka amince da ita a ranar 21 ga watan Maris a birnin Kigali na Rwanda.
Kasar ta yammacin Afrika da aka zaba ta karbi bakuncin sakatariyar yankin a ranar 7 ga watan Yulin bana lokacin da shugabannin nahiyar suka kaddamar da yankin yayin taron AU da aka yi a birnin Niamey na Niger, ta kuma yi alkawarin bada gudumuwar dala miliyan 10 na fara gudanar da ayyukan sakatariyar. (Fa'iza Msutapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China